Zaɓen shugaban ƙasa a Colombia | Labarai | DW | 28.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaɓen shugaban ƙasa a Colombia

Nan gaba a yau ne, a ƙasar Colombia, za a fara zaɓen shugaban ƙasa, tsakanin yan takara guda 6, da su ka haɗa da shugaba mai ci yanzu, Alvaro Uribe, dake karagar mulki tun shekara ta 2002.

Kimanin mutane million27 ne, ya cencenta su kaɗa kuri´a, a runfunan zaɓe dubu 55.

Ƙiddidigar jin ra`ayin jama´a, na nuni da cewar, shugaban Uribe, za shi tazarce, tare da, a ƙalla, kashi 55 zuwa 60,bisaa 100, na yawan ƙuri´un da za a kaɗa.

Sannan wannan alƙulumma na hasashen samun kashi fiye da 50, bisa 100, na jama´ar da za su ƙauracewa zaɓen.

Ƙungiyar yan tawaye, ta Farc mai yawan dakaru dubu 17, ta yi kira ga al´ummomin yakunan da ta ke cikin hannun ta, da cewar, kar su zaɓi shugaba Alvaro Uribe.

To saidai kuma, yan tawayen ,bas u hito hili ba, su ka bayyana ɗan takara da su ke nunawa goyan baya.