Zaɓen shugaban ƙasa a Burkina Faso | Labarai | DW | 20.11.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaɓen shugaban ƙasa a Burkina Faso

Da alamun shugaba Blaise Campaore na Burkina Faso zai lashe zaɓen shugaban ƙasa gobe Lahadi daga cikin ´yan takara shidda .

default

Blaise Compaore shugaban Burkina Faso

A gobe ne idan Allah ya kai mu al'ummar ƙasar Burkina Faso za su  kaɗa ƙuria a zaɓen shugaban ƙasa. Shugaba mai ci yanzu Blaise Compaore na daga cikin 'yan takara shidda da zasu fafata a zaɓen, sai dai ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a na nuni da cewa shugaban mai ci, na iya samun nasarar yin ta zarce a kan karagar mulki.

Da ya ke jawabi da magoya bayansa, Blaise Compaore ya yi alƙawarin kyautata jin daɗin rayuwar al'umma da kuma kawar da talauci.

Tun dai a shekarar 1987 ne Blaise Compaore ya ɗare kujerar shugabancin ƙasar bayan ya kifar da mulkin Thomas Sankara.

Hukumar zaɓen ƙasar ta ce tana fatan bayyana sakamakon zagayen farko na zaɓen a ranar Alhamis mai zuwa.

Mawallafiya: Pinado Abdu

Edita: Yahouza Sadissou Madobi