Zaɓen shugaban ƙasa a Bulgaria | Labarai | DW | 22.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaɓen shugaban ƙasa a Bulgaria

A Bulgaria yau ne, a ke gudanar da zaɓen shugaban ƙasa zagaye na farko.

A jimilce mutane kussan milion 7, za su zaɓen shugaban da zai saka Bulgaria, a jerin ƙasashe membobin ƙungiyar gamayya turai, ranar 1 ga watan januari mai zuwa.

Ƙiddidigar jin ra´ayin jama´a, ta nunar da cewa, bisa dukan alamu, shugaba mai ci yanzu, Gueorgui Parvanov, mai shekaru 49 a dunia za shi tazarce.

A sa ran sakamakon samun sakamon zaɓen, komin dare, a yau lahadi, bayan rufewar runfunan zaɓe a ƙarhe 4 agogon GMT.