Zaɓen shugaban ƙasa a Argentina | Labarai | DW | 28.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaɓen shugaban ƙasa a Argentina

Masu zabe a kasar Argentina sun fara kada kuri´a don zaben sabon shugaban kasa. Ga dukkan alamu dai uwargidan shugaban wato Christina Fernandez de Kirchner ce zata zama mace ta farko da za´a zaba a matsayin shugabar kasa. Binciken jin ra´ayin masu zabe da aka gudanar gabanin zaben na yau yayi nuni da cewa Christina Fernandez mai shekaru 54 kuma ´yar majalisar dattawa tana kan gaba. Ta fi samu goyon baya a tsakanin talakawan kasar, wadanda ke son ganin an ci-gaba da aiwatar da manufofin canje canje da mijinta, wato Nelson Kirchner ya fara. Canje canjen dai sun tayar da komara tattalin arzikin kasar bayan rugujewar sa a shekara ta 2001. Akwai wasu ´yan takara 13 a zaben na yau.