1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zaɓen sabon shugaban Jamus

An Gabatar da sunan Christian Wulff mai shekaru 50 a duniya a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasar Jamus

default

Ɗan Takaran shugaban Ƙasar Jamus Christian Wulff

Bayan murabus daga kujeran shugabancin Jamus da Horst Köhler yayi ba zato ba tsammani, yanzu dai haɗakan jam'iyun dake mulki na CDU da CSU da kuma FDP sun gabatar da sunan Christian Wulff shugaban jam'iyar CDU dake mulki a matsayin ɗan takaransu a zaɓen da za'a gudanar a ƙarshen wannan wata da muke ciki.

Gabatar da sunan Christian Wulff mai shekaru 50 a duniya kuma Firimiyan jihar Lower Saxony a matsayin ɗan takarar jam'iyun  CSU da FDP da kuma CDU na shugabar gwamnati Angela Merkel da kuma ministan harkokin waje kuma mataimakin shugaban gwamnati Guido Wessterwelle, yazo ne bayan da akayi ta  hasashen wanda jam'iyun haɗin guiwan zasu gabatar, musanman idan akayi la'akari da rinjayen da suke dashi a Majalisar dokokin Jamus, lamarin da ake fatan zai baiwa ɗan takakar nasu nasara a zaɓen shugaban ƙasan a ƙarshen wannan wata da muke ciki.

Sai dai kuma gabatar da Wulff a matsayin ɗan takaran jam'iyun ƙawancen mataki ne da sauran jam'iyun adawa na SPD da kuma jam'iyar the Greens dake majalisan dokokin na Jamus sukayi suka a game dashi.

A ɓangaren jam'iyun adawan dai sun gabatar da sunan Joachim Gauck, mai shekaru 70 kuma wani sasannen ma'aikacin wata hukumar binciken gwamnati daya shafe shekaru  goma yana gudanar da bincike akan takardun bayanan asiri akan aika-aikan da gwamnatin kwaminis ta tsohuwar Jamus ta gabas ta aikata.

Frank-Walter Steinmeier im Bundestag

Shugaban 'Yan adawa Frank-Walter Steinmeier

A cewar shugaban jami'yar adawa ta SDP kuma tsohon ministan harakokin waje Frank Walter Steinmeier wannan zaɓi bazai taimakawa gwamnati ba:

Yace "Ina mamaki game da irin wannan hali da jam'iyun dake mulki suka ɗauka na ƙin amincewa da tayin da mukayi masu na zaɓen wani mutum guda da bashi da alaƙa da jam'iya domin samun ɗokacin goyon bayan wakilan majalisar dokokin Jamus akan wannan muƙami"

 To sai dai kuma a ɓangarenta shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayyana Wolff a matsayin mutumin daya kamata dokacin yan majlisar suyi na'an dashi:

tace"Ina son na gabatar maku da christian Wolff a matsayin shugaban Jamus. Mutun ne dana sani tun lokacin da ake gwagwarmayan haɗewar Jamus, kuma mutum ne mai son jama'a da sanin yakamata a duk wani aiki da ya sa a gaba, kuma kamilin mutum ne dake zama abin misali wanda ya dace ya zama shugaban Jamus.

Shima da yake kare kansa game da cancantar sa game da takaran wannan mukami, Christian Wolff cewa yayi: Ina ganin mutum yana iya zama jagoran mutane kuma tare da haɗa kan al'umma ta hanyan baiwa al'umma ƙwarin guiwa a lokacin da suka samu kansu cikin wani hali mai wahala.

Yanzu dai masu sharhi akan harkokin siyasar Jamus na ganin rashin samun daidaito tsakanin jam'iyun adawa da kuma masu riƙe da mulki zai iya haifar da zaɓe mai zafi, wanda kuma ake ganin jam'iyun adawa zasu so samun goyon bayan wasu 'yan siyasan na ɓangaren masu mulki wajen mara ma nasu ɗan takaran baya, wanda ake ganin bashi da alaka da wata jam'iya.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Yahouza Sadissou Madobi