Zaɓen raba gardama a Turkiya | Labarai | DW | 12.09.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaɓen raba gardama a Turkiya

An fara kaɗa ƙuri'ar raba gardama a Turkiya da zai bai wa ƙasar damar kwaskware kundin tsarin mulkinta ko a'a.

default

Kaɗa ƙuri'a a Turkiya

A Turkiya, an buɗe runfunan zaɓe a sassa daban daban na ƙasar domin bai wa mutane miliyon biyar 'yancin kaɗa kuri'a a zaɓen raba gardama da zai bayar da damar kwaskware kundin tsarin mulkin ƙasar koko a'a. Ƙididdigar jin ra'ayin jama'a da aka gudanar a baya-bayannan ta nunar da cewa 'yan ƙasar za su amince da sauye-sauyen dokoki 26 na kundin da gwamanti ta yi, domin sun fi dacewa da manufofin demokaraɗiya da kuma muradun ƙasashen yammacin duniya.

Ƙungiyar Gamayyar Turai ta yaba da wannan mataki na gwamantin Ankara. Sai dai ta soki lamarin firaminista Recep Erdogan na rashin bayar da damar tafka mahaawar domin fahimtar da al'uma alƙiblar da ƙasar ta dosa. Masu adawa da kwaskware kundin tsarin mulkin sun nunar da cewa, kwaskwarimar zata karkata aƙalar da aka ɗora Turkiya akai, ta kasa mai bin addinai da dama.

wannan zaɓen jin ra'ayin jama'an ya zo ne a daidai lokacin da ministocin harkokin waje na kasashe da ke da kujera a EU suke nazarin yiwuwar shigar da Turkiya cikin wannan gamayya. Sai dai kuma ƙasashen Syprus ko Chypre, da Faransa da kuma Jamus na ci gaba da hawa kan kujerar na ƙi game da bai wa Turkiya kujera a EU.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Mawallafi: Ahmed Tijjani Lawal