Zaɓen raba gardama a Roumania. | Labarai | DW | 19.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaɓen raba gardama a Roumania.

Watanni 5 bayan shigar ta, a sahun ƙasashen ƙungiyar gammaya turai, yau ne,ƙasar Roumania, ke shirya zaɓen raba gardama , domin baiwa jama´a damar bayyana ra´ayoyin su, a kann batun tsige shugaban ƙasa Traian Basescu.

Fiye da mutane milion18 ya cencenta su kaɗa ƙuri´u a, inda za su amsa tambayar da ke rubuce a katocin zaɓe, ta cewar: shin kun amince a tsige shugaban ƙasa.

An zabi shugaban Tarian Basecu a matsayin ƙasar Roumania, tun shekara ta 2004, amma a watan Aprul da ya gabata, yan majalisar dokoki su ka sauke shi daga muƙamin sa, bayan sun zarge sh,i da yin karan tsaye, ga kundin tsarin mulki.

Kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanada, bayan yan majalisun dokoki sun sauke shugaban ƙasa, jama´a ke da wuka da nama, wajen tabbatar da wannan hukuci ko kuma akasin haka, ta fannin kaɗa ƙuri´a.

Tun bayan tsige shugaban ƙasar, daga wannan muƙami shugaban majalisar dattawa ke riƙe da matsayin shugaban ƙasar wucin gadi.

Nan gaba a yau za a bayyana sakamakon wannan zaɓe.