1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaɓen majalisun dokoki a Kyrgzstan

An fara kaɗa kuri´u a ƙasar Kyrgzstan, don zaɓar sabbin ´yan majalisun dokoki. Matuƙar ba ´ayi hankali ba zaɓen a cewar rahotanni ka iya buɗe sabon babin rikicin siyasa a ƙasar. Jam´iyyun adawa dai sun zargi shugaba Kurmanbek Bakiyev da ƙoƙarin shirya yin maguɗi a zaɓen. Ɓarkewar rikici a Kyrgzstan babban ƙalubale ne ga ƙasashen Amirka da kuma Russia. A yanzu haka dai ƙasashen biyu na da cibiyar tsaro da su ka girke a wannan ƙasa.