Zaɓen jihohi a ƙasar Faransa | Siyasa | DW | 22.03.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zaɓen jihohi a ƙasar Faransa

Jam´iyar UMP ta shugaba Nicolas Sarkozy ta sha kayi a zaɓen jihohin ƙasar Faransa

default

Nicolas Sarkozy ya sha kayi a zaɓen jihohi

Jam´iyar PS a ƙasar Faransa ta samu nasara a zagaye na biyu na zaɓen jihohi da aka gudanar a jiha lahadi

A sakamakon da ofishin ministan cikin gida ya baiyana ya nuna cewa jam'iyyar ´yan gurguzu  suna da kishi 54.15 cikin ɗari yayin da jam'iyar dake mulki ta shugaba Nikola Sarkozy ke da kishi 35,39 cikin ɗari na ƙuri´un da aka kaɗa

Wannan mummuna kayi da jam iyar ta Sarkozy ta sha tun can da ma babu wani mamaki da ake da shi dangane da yadda tun a zagaye na farko ´yan gurguzun suka yi nasara a jihohi da dama

Ko da shi ke jam´iyyar dake mulkin ta sha kashi a yanukunan da dama to amma duk da haka a jihohi kamar su Alsace da Guyane da Reunion jam'iyar ta UMP ta yi nasara

 An gana tsakanin shugaban ƙasa Nicolas Sarkozy da Firaminista Francois Fillon wanda shine ya jagorancin yaƙin neman zaɓen inda suka tattauna  butun garambawul  na majalisar ministocin.

Yanzu haka akwai  rahotanin da ba a tabbatar da gaskiyarsu ba dake nuna cewa wasu ministocin menbobin jam´iyar ta UMP sun fara murabus a sakamakon kaye da jam´iyyar ta sha wanda aka ƙiyesta cewa mimistocin 20 na jam´iyyar dake mulki suka tsaya takara a zaɓen  kana suka sha kaye a yankunan daban daban

Waɗanda ke kusa da Firaministan sun ce shi kame ko kadɗn ba zai yi marabus ba daga masayin

 da ya ke Magana akan zaɓen  Firaministan Francoi Fillon ya ce:

Ba mu shawo kan jama´a ba su amince su yarda  da mu,wannan na zaman kaye garemu ´yan jamiyyar UMP kuma ni da kaina na ɗauki alhakin rashin samun nasara a wannan zaɓe kuma zamu tattauna da shugaban ƙasa.

Yan gurguzun dai waɗanda suke da rinjaye a zaɓen tare da sauran jam´iyyun siyasar masu neman sauyi sune ke riƙe da kusan kishi biyu cikin ukku na jihihohin da ake da su a Faransa

Babbar magatakarda ta jam´iyar PS Martin Aubry ta ce zasu cikka alƙawarin da suka ɗauka ga jama´a:

Tun daga gobe zamu fara aiki a cikin jihohinmu, kuma za mu cikka alkawarin da muka ɗauka tun lokacin yaƙin neman zaɓe kan samar da aiki da kula da makomar matasa.

Wannan kaye dai da jam´iyar ta UMP ta sha ,na zaman abinda masu lura da al´ amuran siyasa ke kallon mataki na farko na faɗuwar jam`'iyar a zaben shugaban ƙasa da za a yi a shekara ta 2012

Ko da shike shugabanin jam´iyyar sun bada tabbacen cewa zasu ɓullo da sabon salon a zaɓuɓukan tafe masu fashin baki akan al amuran siyasa na hasashen cewa taɓargazan shugaba Sarkozy itace ta jayomasa wannan kaye

Namiam Frank wani mai yi sharhi ne aka al´amuran siya a ƙasar ta Faransa:

Kuskuren shugaba Sarkozy shine ummal iba´isar  abin da suka girbe a yau.

Ana iya yin sauye sauye a kowace ƙasa amma wasu sauye saune dolene a yi watsi da su idan yan ƙasa ba su gamsu da su ba.

Mawwallafi: Abdourahman Hassane Edita: Yahouza Sadissou Madobi