Zaɓen gama gari a Belgium | Labarai | DW | 13.06.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaɓen gama gari a Belgium

An fara kaɗa ƙuri' a a Belgium daidai lokacin da ake fargabar rabewar ƙasar

default

Shugaban jam'iyar NVA, New Flemish Alliance Party, Bart De Wever, mutumin da ake ganin shi zai zama sabon Firamninistan ƙasar. Yana goyon bayan raba ƙasar

A yau ake gudanar da zaɓen gama gari a ƙasar Belgium. Masu zaɓe za su yanke hukunci akan makomar wannan ƙaramar ƙasa wadda al'ummar ta masu magana da harshen Dutch miliyan 6.5 da masu magana da harshen Faransanci miliyan huɗu ke nuna rashin jin daɗinsu ga zaman tarayya. Ana sa ran cewa babbar jam'iyar 'yan Flemish dake neman ɓallewa tare da 'yan Dutch zuwa tarayyar Turai, za ta taka rawar gani. Har in ta faru to hakan na nufin babban koma-baya ga 'yan Wallonia wato al'ummar kudancin Belgium masu magana da harshen Faransanci, waɗanda talakawa ne da suka dogara kan tallafi daga yankin 'yan Flemish. An dai kira wannan zaɓe na gaba da wa'adi ne bayan rushewar jam'iyar ƙawance ta Firaminista Yves Leterme a cikin watan Afrilu sakamakon wata taƙaddama game da wata mazaɓa ta masu amfani da harsuna guda biyu.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Yahouza Sadissou Madobi