Zaɓen farko a Guinea bayan shekaru 50 | Labarai | DW | 27.06.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaɓen farko a Guinea bayan shekaru 50

Ban ki-moon yayi kiran da a gudanar da zaɓen cikin haske da adalci.

default

Shugaba Sekouba Konate na Guinea

Jama'a da dama ne suka fito domin kaɗa ƙuri'un zaɓen shugaban ƙasa na farko a Guinea wanda ake fatan zai kawo ƙarshen mulkin kama karya na Soji da fararen hula da aka kwashe shekaru fiye da hamsin ana yi a ƙasar.

Kimanin masu zaɓe miliyan huɗu ne, ake fatan zasu kaɗa ƙuri'a a zaɓen na yau, wanda ´yan kallo na ƙasashen waje ke saka ido akai.

A jawabinsa shugaban gwamnatin mulkin sojan ƙasar Janar Sekouba Konate, yace zaɓi ya ragewa 'yan ƙasar na zaɓen 'yanci da zaman lafiya da demokiraɗiyya ko kuma tashin hankali.

A ɓangaren sa babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Ban ki-moon yayi kiran da a gudanar da zaɓen cikin haske da adalci.

A sanarwar Ban ki-moon ya bayyana fatan zaɓen wanda shine na farko cikin shekaru fiye da Hamsin, zai kasance abin misali ga sauran ƙasashe na Afirka.

Yanzu haka dai akwai 'yan takara 24 dake takaran mukamin na shugaban ƙasa.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Yahouza Sadissou Madobi