Zaɓen Congo zai kai ga zagaye na biyu | Labarai | DW | 21.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaɓen Congo zai kai ga zagaye na biyu

A ƙasar Jamhuriyar dimokraɗiyar Congo zaá doshi zagaye na biyu na zaɓen shugaban ƙasa bayan da dukkanin yan takarar suka gaza samun rinjayen kashi 50 cikin ɗari na adadin ƙuriún da aka kaɗa. Shugaban ƙasar mai ci a yanzu Joseph Kabila ya zo dab da kashi 45 cikin ɗari na kuriún, yayin da babban abokin hamaiyar sa kuma mataimakin shugaban ƙasar kana madugun yan tawaye Jean-Pierre Bemba yake da kashi 20 cikin ɗari na adadin kuriún. Yan takarar biyu za su ƙalubalanci juna a zagaye na biyu na zaɓen wanda aka shirya gudanarwa a ƙarshen watan Oktoba. Zaɓen shugaban ƙasar dana yan Majalisun dokoki da aka gudanar a ranar 30 ga watan Yulin da ya gabata, shi ne zaɓe karo na farko bisa tsarin jamíyu da dama wanda ya gudana a tsawon shekaru fiye da 40 a tarihin ƙasar Congo. A halin da ake ciki kuma an bindige wani soja har lahira wanda ke nuna goyon baya ga Jean Pierre Bemba a yayin musayar wuta da dogarai masu tsaron lafiyar shugaba Joseph Kabila a kusa da ofishin hukumar zaɓen dake Kinshasa babban birnin ƙasar.