1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zaɓen ƙasar Holland

A zaɓen majalisar dokoki a ƙasar Holland da za a gudanar a ran laraba, 22 ga watan Nuwamba, sakamakon wani binciken jin ra’ayin jama’a da aka gudanar na nuna cewa, a kwananin bayan nan, Firamiyan ƙasar ya yi ta ƙara samun goyon baya, abin da ke nuna cewa, hakan zai iya sa ya lashe zaɓen.

A cikin ’yan watannin da suka wuce, lokacin da majalisar dokokin ƙasar Holland ta ka da ƙuri’ar ƙin amincewa da gwamnatin Firamiya Jan-Peter Balkenende, kowa ya yi ta zaton cewa, ƙarshen aikinsa ke nan a fagen siyasa. Masharhanta da dama na ƙasar sun fi mai da hankalinsu ne kan abokin hamayyar Firamiyan, Wouter Bos, na jam’iyyar adawa ta Socialdemocrats, wanda a lokacin ake ganin kamar shi ne zai iya yi wa duk kurakuran da Firamiyan ya yi a ƙasar gyara. Amma sai ga shi tun ’yan kwanaki kaɗan kafin ranar zaɓen ta yau, binciken jin ra’ayin jama’a na nuna cewa, mafi yawansu sun sake nuna goyon bayansu ne ga Firamiya Balkenede. Batutuwan da suka fi jan hankulla a yanzu, sun shafi harkokin cikin gida ne da na tattalin arziki. Ba kamar a lokacin da majalisar ta janye goyon bayanta ga gwamnatin ba, inda al’amuran harkokin waje suka fi mamaye ra’ayin jama’a. Hakan kuwa ya bai wa Firamiyan ƙarfin gwiwa, a yaƙin neman zaɓe. A wata muhawarar da suka yi a kan talabijin da abokin hamayyarsa Wouter Bos, cewa ya yi:-

„Babu shakka: ina amanna da ra’ayoyin Wouter Bos, tamkar ɗan Adam, kuma a matsayinsa na ɗan siyasa. Amma idan aka zo ga batun tafiyad da harkokin zamantakewa a nan Holland, to na fi yarda da kaina.“

Tun lokacin rushewar gwamnatinsa a lokacin bazara ne Firamiyan ke jagorancin gwamnatin riƙon ƙwarya, wadda ke tafiyad da harkokin yau da kullum na ƙasar Holland ɗin, kafin a gudanad da zaɓe. A cikin wannan lokacin ne dai kuma, aka sami bunƙasar tattalin arzikin ƙasar, yayin da yawan marasa aikin yi kuma ya yi ƙasa zuwa kusan kashi 5 cikin ɗari. Masharhanta da sauran jama’an ƙasar na ganin wannan sauyin ne tamkar sakamamkon da matakan da Firamiya Balkenende ya ɗauka suka haifar. A cikin matakan kuwa, har da soke dokar nan da ke bai wa jama’a damar zuwa pansho da wuri, da kuma rage tallafin da ake bai wa marasa aikin yi, tare da bai wa kafofin kiwon lafiya damar yin tserereniya tsakaninsu. Game da sakamakon da Firamiya Balkenende ya samu dai, shugaban gwamnatin tarayyar Jamus Angela Merkel, a lokacin ziyarar da ta kai a ƙasar Holland ɗin, ta ce wannan abin kwaikwayo ne ga ƙasarta. Sai dai tsarin na da kuma illolinsa, kamar yadda ’yan jam’iyyar adawar ƙasar ta Socilademocrats ke bayyanarwa. Da farko dai, ɗan takaran jam’iyyar, Wouter Bos, ya yi Allah wadai da shirin ne saboda a nasa ganin, yana ta ƙara haɓaka giɓin da akwai ne tsakanin mawadata da talakawan ƙasar. Kamar dai yadda ya bayyanar:-

„Shirin ya sa tsoffin mutane na ganin kansu ne tamkar ba su da wata daraja kuma, sai ma janyo matsaloli kawai suke yi ga jama’a. To burinmu ne mu canza wannan matsayin a shekara mai zuwa. Bai kamata mu yi ta ganin tsoffin mutane tamkar wata matsala gare mu ba. Sun cancanci su sami daraja da kuma ’yancin iya tsufa tsakaninmu.“

Wannan matsayin da Bos ya ɗauka dai, ya janyo wa jam’iyarsa farin jini a bainar jama’a. Amma a kan batun haraji ne, ra’ayoyin magoya bayan jam’iyyar suka bambanta.

A zahiri dai, masharhanta na ganin cewa, jam’iyyar Social Democrats ɗin ba za ta iya lashe wannan zaɓen ba. Kazalika kuma, jam’iyyar Liberals ma ba za ta taɓuka kome ba a zaɓen, idan aka yi la’akari da sakamakon binciken da aka gudanar na jin ra’ayin jama’a.

 • Kwanan wata 22.11.2006
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BtxL
 • Kwanan wata 22.11.2006
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BtxL