Zaɓe ya ƙarato a France | Labarai | DW | 18.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaɓe ya ƙarato a France

Yan takara neman shugabancin ƙasar Fransa, sun shiga gangarar ta ƙarshe a yaƙin neman zaɓe.

Ya zuwa yanzu daga yan takara 12 da ke buƙatar maye gurbin shugaba Jaquces Chirak , 4 a ke kyauttata zatan za su taka rawar gani a zagayen farko, na zaɓen da za a gudanar ranar lahadi mai zuwa.

Wannan yan takara sun haɗa da, Nikola Sarkozy na jami´ yar UMP, mai riƙe da ragamar mulki, sai kuma Segolene Royal ta Jam´iyar PS, na ukun,su shine, Fransois Bayrou na jam´iyar FDN mai matsakaicin ra `ayi, sannan Jean Marie Le Pen, na jam´iyar FN mai aƙidar nuna ƙyamar baki, wanda wani mataki na ba zata, ya kara a zagaye na 2, tare da shugaba mai barin gado Jaques Chirac a zaɓen shekara ta 2002.

Sanarwa daga opishin ministan cikin gida, a birnin Paris, ta bayyana cewar, komai ya kammalla a shirye-shiryen wannan zaɓe, hatta a ƙasashen ƙetare, inda kussan Fransawa dubu ɗari 9, za su kaɗa ƙuri´a.