Zaɓe gaba da waádi a ƙasar Turkiya | Labarai | DW | 02.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaɓe gaba da waádi a ƙasar Turkiya

P/M Turkiya Tayyip Erdowan ya buƙaci gudanar da zaɓen gama gari gabanin lokaci domin sasanta taƙaddama da yan adawa ta tsame addini daga harkokin gwamnati. Mai yiwuwa ne a gudanar da zaɓen a ranar 24 watan Yuni. Bugu da kari P/M ya sasanar da cewa zai gabatar da wani gagarumin garanbawul ga shaánin zaɓen wanda zai haɗa da bawa yan ƙasar damar zaɓen shugaban ƙasa kai tsaye. Erdowan wanda ke shugabantar jamíyar AKP mai mulki ya sanar da waɗannan matakan ne bayan da kotun tsarin mulki ta Turkiyan ta soke zagayen farko na zaɓen shugaban ƙasa da yan majalisar dokokin suka gudanar a makon da ya gabata. Jamíyun adawa waɗanda babu ruwan su da addini sun shigar da ƙara a gaban kotun domin hana Ministan harkokin wajen ƙasar Abdullahi Gul ɗan jamiyar AKP ne tsayawa takarar neman shugabancin ƙasar. Takarar sa ta haifar da musyar raýi mai zafi a Turkiya inda wasu ke zargin cewa yan da wata ajanda ta addini a ɓoye a cikin zuciyar sa.