Zaɓe a Jamhuriya Demokradiyar Kongo | Labarai | DW | 01.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaɓe a Jamhuriya Demokradiyar Kongo

Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Jamhuriya Demokradiya Kongo, ta tsaida ranar 30 ga watan July, domin shirya zaɓen shugaban ƙasa da na yan majalisun dokoki.

Da farko an tsara gudanar da wannan tagwayen zaɓuka ranar 18 ga watan juni, amma a ka ɗage, dalilin rashin cimma daidaito, tsakanin jam´iyun siyasa, da kuma rashin kamalla tsari a lokaci.

Wannan zaɓuka, su ne na farko ,tun bayan da ƙasar ta samu yancin kanta, daga turawan mulkin mallaka na ƙasar Belgium, sannan za su dassa aya, ga mulkin riƙwan ƙwarya, da a ka girka a ƙasar tun shekara ta 2003, a sakamakon yaƙe yaƙe, da su ka hadasa mutuwar mutane a ƙalla million 4, a ƙasar da ƙasashe maƙwabtan ta.

Za a fara yaƙin neman zaɓe ranar 29 ga watan yuni.

Hukumar zaɓe ta bayyana amincewa, da yan takara 33,a zaben shugaban ƙasa, da su ka haɗa da shugaba riƙwan ƙwarya Joseph kabila.

Sannan kotun ƙoli ta ƙasa, na ci gaba da tace yan takara, kussan dubu 10, da ke bukatar shiga majalisar dokoki, da ta ƙunshi yan majalisa 500.