Zaɓe a Amurika | Labarai | DW | 07.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaɓe a Amurika

A ƙalla Amurikawa milion 200, za su gudanar da zaben yan majalisun dokoki da gwamnanon jihohi a ranar yau talata.

Ƙiddigar jin ra ´ayin jama´a, da a ka gudanar, na nuni da cewa, bisa dukkan alamu, yan jama´iyar Democrate, za su lashe wannan zaɓe, kasancewar mafi yawan Amurikawa, sun dawo daga rakiya jam´iyar Republican, ta la´akari da tabargazar da shugaba Georges Bush ya tabka, a game da batun yakin kasar Iraki.

Masu nazarin harajkokin siyasa a Amurika na dangata wannan zabe a matsayin kuri´a jin ra´ayin jama´a, a game da mulkin Georges Bush.

Savbuwar majalisar da za a zaɓe ya zata fara mulki a watan janairu mai zuwa.

Shugaban Amurika, da ya shiga wani hali na tsaka mai wuya, ya yi kira ga Amurikawa, su ci gaba da bashi amana, ta hanyar zaɓen yan takara jam´iyar Republican.

Kwana ɗaya kamin gudanar da zaɓen, wasu gungun sojojin Amurika, sun hiddo ƙasida, inda su ke bukatar sa hannun sauran takwarorin su, na yin Allah wadai, ga yaƙin Irak.