Zaɓe a ƙasar Hongrie | Labarai | DW | 23.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaɓe a ƙasar Hongrie

A ɗazunan ne, a cen ƙasar Hongrie, a ka fara zaɓen yan majalisun dokoki zagaye na 2.

A zagayen farko, da a aka gudanar ranar 9 ga watan da mu ke ciki, jam´iyar yan gurguzu, ta Praminista mai ci yanzu, Ferenc Gyurcsany ,tare da abokan ƙawancen ta, sun tattara yawan ƙuri´u da su ka basu damar, samun kujeru 113, daga jimmilar kujeru 386, da majalisar dokokin ƙasar ta ƙunsa.

A nata ɓangare jam´iyar adawa, ta tsofan Praminista Victor Orban, ta haɗa kujeru 97.

Masharahanta a ƙasar na nuni da cewar, akwai alamun jam´iya mai ci yanzu, ta samu tabaraki, daga al´ummar ƙasa.

Idan hakan ta tabata, wannan shine karo na farko, da jam´iyar da ke riƙe da ragama mulki ,ta samu nasara yin tazarce, tun farkon demokraɗiya a ƙasar Hongrie a shekara ta 1990.

Hongrie na ɗaya daga ƙasashen da su ka shiga ƙungiyar gamayya turai, a baya bayan nan, sannan ta na sahun ƙasashe masu raunin tattalin arziki a nahiyar turai.