Zaá dagewa hukumar falasdinawa takunkumi idan......... | Labarai | DW | 13.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaá dagewa hukumar falasdinawa takunkumi idan.........

P/M Britaniya Tony Blair ya buƙaci dagewa hukumar gudanarwar falasdinawa takunkumin tattalin arziki idan sabuwar majalisar gudanarwa ta haɗin kan ƙasa da zaá kafa ta cika kaídojin ƙasa da ƙasa. Jamián Falasɗinawan na fatan sabuwar gwamnatin da zaá kafa zata share fagen ɗage takunkumin tsukewa hukumar gudanarwar falasɗinawan bakin aljihu, wanda aka ƙaƙaba mata tun bayan da Hamas ta kafa gwamnati a watan Maris na wannan shekarar.