1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓen zakaran gwajin dafi a ƙasar Kenya

Ibrahim SaniDecember 25, 2007
https://p.dw.com/p/CgAB

Kafafen yaɗa labarai sun rawaito Shugaban jam´iyyar adawa a ƙasar Kenya Raila Odinga, na cike da fatan lashe zaɓe na shugaban ƙasa. Zaɓen da za a fafata, a tsakanin sa da shugaba mai ci wato Mwai Kibaki, zai gudana ne a jibi alhamis idan Allah ya kaimu. Mr Odinga ya tabbtar da cewa karɓuwar da Jam´iyyarsu take da shi a tsakanin al´umman ƙasar, alamace ta samun nasara a wannan zaɓe. Kuri´ar jin ra´ayin jama´a ta nunar da cewa, Mr Odinga ya bawa Mwai Kibaki rata yar ƙalilan. Tuni `yan sanda su ka ɗauki tsauraran matakan tsaro, kafin zuwan lokacin wannan zaɓe. Rahotanni sun ce zaɓen ´yan majalisun dokoki dana kawunsiloli, zai gudana ne rana ɗaya dana shugaban ƙasa. A Jawabansu na Sallar Kirsimeti Shugabannin addinai na ƙasar, sun buƙaci al´umma zaɓar wanda ya cancanta a tsakanin´ yan takarar biyu.