1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓen shugaban ƙasa da na yan majalisun dokoki a Uganda

February 23, 2006
https://p.dw.com/p/Bv72

Yau ne al´ummar ƙasar Uganda ke gudanar tagwayen zaɓe, na shugaban ƙasa zagaye na farko, da na yan majalisun dokoki.

Wannan shine karo na farko ,tun shekaru 26 da su ka wuce, da ƙasar Uganda, ke shirya zaɓe, bisa tafarkin demokraɗiyya.

A zaɓɓuɓɓukan da su ka gabata , yan takara, na ajje takara, ba ƙarƙashin tutuar jam´iyun siyasa ba.

A baki ɗaya, mutane million10 da rabi, za su zaɓi ɗaya daga yan takara 5, da su ka shiga gwaggwarmayar neman shugabancin wannan ƙasa.

Yan takara sun haɗa da shugaban mai ci yanzu ,Yoweri Museveni, da ke kan karagar mulki tun shekara ta 1986, wato shekaru 20 kenan ,da su ka shuɗe.

ƙiddidigigar neman jin ra´ayin jama´a , ta bayyana cewar shugaba Yoweri za shi tazarce.

A nasu gefe,tunni yan adawa sun fara ƙorafin shirya magudi.

Ya zuwa yanzu, rahotanin daga Kampala baban birnin kasar, sun shada cewar zaɓen na wakana lami lahia, duk da yan matsaloli da aka fuskanta, a lokacin kampen.