Zaɓen shugaban ƙasa a Rwanda
August 9, 2010Talla
A yau ne ƙasar Rwanda ke gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da ke zama irinsa na biyu tun bayan yaƙin basasa da ƙasar ta fiskanta a shekarar 1994. Duk da cewa 'yan takara uku ne ke ƙalubalantar Paul Kagame mai shekaru 52 da haihuwa, amma kuma manazarta sun yi hasashen cewa shugaba mai barin gado zai samu damar sabonta wa'adin mulkinsa na shekaru bakwai.
Shi dai Paul Kagame da ya kafa jam'iyar FPR ya ɗare kan karagamar mulki shekaru 16 da suka gabata, bayan da masu tsattsauran ra'ayi na ƙabilar Hutu suka aiwatar da kisan ƙare dangi a kan mutane dubu 800 na ƙabilar shugaban wato Tutsi. Mutane miliyan biyar ne suka yi rajista a ƙasar ta Rwanda domin kaɗa kuri'unsu a zaɓen na yau.
Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Mohammad Nasiru Awal