1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓen shugaban ƙasa a Ivory Coast

October 30, 2010

Fatan samarda Demokraɗiyya mai ɗorewa da zaman lafiya a ƙasar da ke fama da rigingimun 'yan tawaye.

https://p.dw.com/p/Pufc
Laurent GbagboHoto: AP

A yau ne al'ummar ƙasar Ivory Coast ke  kaɗa ƙuri'unsu a karon farko sama da shekaru goma ta ƙasar ta faɗa cikin rigingimun 'yan tawaye daya dare ta zuwa ɓangarori biyu. 'Yan Ivory Coast ɗin dai na fatan cewar wannan zata zame musu wata dama na samarwa da wannan ƙasa da ke yankin yammacin Afirka makoma ta gari a demokradiyance.

Zaɓen na yau dai na kasancewa fatan al'ummar ƙasar na samun haɗin kai a karon farko tun bayan yaƙin shekarata 2002-3 daya dare ƙasar biyu, inda arewaci ya kasance a hannun 'yan tawaye, a yayinda kudanci ya ke karkashin gwamnati. Nasarar wannan zaɓe dai zai sake bawa wannan ƙasa darajarta da kima, musamman a matsayinta na cibiyar kasuwanci da kuma wadda tafi kowace ƙasa albarkatun Koko.

Manazarta dai sun shaidar da cewar samun nasarar wannan zaɓe zai sake buɗewa Ivory Coast din kofarta wa masu zuba jari daga ketare, wanda zai jagoranci inganta harkokin sadarwa da gine-gine, wanda zasu jagoranci sauyin da zai farfaɗo da harkokin kasuwancinta  na samar da   kashi 40 daga cikin 100 na Koko  da Duniya ke bukata.

Alassane Ouattara
Alassane OuattaraHoto: AP

Suma tsoffin 'yan tawayen dai sun gaji da rigingimun da Ivory coast ke fama dashi, kamar yadda Conel Sinima Bamba dake shugabantar cibiyar tsoffin sojojin tawaye da ke Bouake ya yi nuni dashi. Wanda a cewarsa  ya zamanto wajibi a kawo ƙarshen rikicin da ƙasar ke fama dashi, don haka wannan zaɓe yana da matuƙar muhimmanci.

" Dukkanninmu anan muna muradin abu guda. Wannan rikicin ya ishe mu, faɗan bai wuce shekara guda kachal ba, amma yanzu shekaru 8 kenan bayansa. Mun gaji da wannan yanayi. Kuma mun gaji da yadda ake ta sauya lokacin gudanar da zaɓen."

A zaɓen na yau dai shugaba Laurent Gbagbo na takara da tsohon shugaban ƙasar Henri Konan Bedie, wanda ya mulki Ivory Coast daga 1993 zuwa lokacin da aka kifar da gwamnatinsa  a 1999, da Alassane Ouattara daga arewacin ƙasar, mutumin da kuma aka hana shi takara a zaɓuɓɓuka biyu da suka gabata, akan cewar ba ɗan asalin ƙasar bane.

Rahotanni sun shaidar da cewar sakamakon zaɓen dai zai kasance mai sarƙaƙƙiya, dangane da rashin mai samun rinjaye ƙuri'u kai tsaye, kamar yadda aka fuskanta a zaɓuɓɓukan shugaban kasa da suka gabata sau biyu. Sai dai jami'an Majalisar Ɗunkin Duniya da na ƙasashe masu faɗa aji, na cigaba da matsin lamba wa 'yan takarar na su gaggauta amincewa da sakamakonsa, tare da kaucewa ikirarin samun nasara da wuri. Rashin samun ɗan takara mai rinjayen ƙuri'u da zai bashi damar lashe zaɓen, zai jagoranci zuwa zagaye na biyu a karshen watan Nuwamba.

Elfenbeinküste Bedie Besser
Henri konan BedieHoto: DW

Sai dai har yanzu manazarta na cigaba da dasa ayar tambaya dangane da yiwuwar samun zaman lafiya a wannan ƙasa. Jean Louis Billion, shine shugaban hukumar ciniki da masana'antu na Ivory Coast

" Idan muka yi nazari, zamu ga cewar  mun cimma yarjejeniyoyin zaman lafiya fiye da na yaƙe-yaken Duniya guda biyu da suka gabata. Amma har yanzu bamu cimma warware matsalolinmmu ba. Adangane da haka ne nake shakkun cewar, ko 'yan siyasar mu na muradin a kawo ƙarshen rikicin da gaske. Idan muna muradin yin zaɓe, to babu shakka zamu gudanar dashi".

Tuni dai shugaba Laurent Gbagbo ya shaidar da cewar, zaɓen baya razana shi ko kaɗan, sai dai yadda Jam'iyyu da magoya bayansu zasu yi martani dangane da sakamakonsa.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar

Edita:           Abdullahi Tanko Bala