Zaɓen shugaban ƙasa a Burkina Faso
November 20, 2010A gobe ne idan Allah ya kai mu al'ummar ƙasar Burkina Faso za su kaɗa ƙuria a zaɓen shugaban ƙasa. Shugaba mai ci yanzu Blaise Compaore na daga cikin 'yan takara shidda da zasu fafata a zaɓen, sai dai ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a na nuni da cewa shugaban mai ci, na iya samun nasarar yin ta zarce a kan karagar mulki.
Da ya ke jawabi da magoya bayansa, Blaise Compaore ya yi alƙawarin kyautata jin daɗin rayuwar al'umma da kuma kawar da talauci.
Tun dai a shekarar 1987 ne Blaise Compaore ya ɗare kujerar shugabancin ƙasar bayan ya kifar da mulkin Thomas Sankara.
Hukumar zaɓen ƙasar ta ce tana fatan bayyana sakamakon zagayen farko na zaɓen a ranar Alhamis mai zuwa.
Mawallafiya: Pinado Abdu
Edita: Yahouza Sadissou Madobi