1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

200510 Äthiopien Parlamentswahl VB

May 21, 2010

Zaɓen zai kasance zakaran gwaji dafi na wanzuwar dimokraɗiya a ƙasar.

https://p.dw.com/p/NUXz
Babban taron gangami na Jam'iyar EPRDF ta ƙasar Ethiopia.Hoto: DW

A ranar lahadin nan mai zuwa ce al'umar ƙasar Ethiopia za su fita domin kaɗa ƙuri'a a zaɓen majalisun dokoki. Wannan zaɓen dai zai kasance zakaran gwajin dafi bayan tarzomar da biyo bayan rikice rikicen da suka faru a zaɓen shekarar 2005 wanda janyo hasarar rayukan mutane kimanin 200. Bugu da ƙari zaɓen zai fayyace ko ƙasashe masu bada taimakon jin ƙai za su cigaba da bada tallafin da suka dakatar ko kuma a'a kuma ko ƙasar ta Ethiopia za ta cigaba da taka rawar gani a yankin na ƙahon Afrika.

Yan adawa dai da ƙungiyoyin kare haƙƙin bil adama sun zargi jam'iyar dake mulkin ƙasar tun shekarar 1991 wato EPRDF da murɗiya da kuma tursasa jama'a.

Zirga zirgar ababen hawa da akan ji a dandalin Meskel dake tsakiyar birnin Addis Ababa babban birnin Ethiopia. An sanya wani dagi mai hoton zuma dake zama alamar Jam'iyar ƙasar mai mulki wadda Firaminista Meles Zenawi ke jagoranta. Alamar ta ƙudan zuma na matsayin ƙwazo, jajircewa da aiki tuƙuru domin ciyar da ƙasar gaba.

Wahlkampf Äthiopien 2010
Magoya baya sanye da riguna ɗauke da hoton Firaminista Meles ZenawiHoto: DW

Sai dai a waje guda yan adawa basu manta da irin tursasawar da aka yi musu ba a shekarar 2005 da ɗaurin da aka yiwa wasunsu a gidan yari har ma da 'yan jaridu da suma suka ɗanɗana kuɗarsu da dokokin kama karya da gwamnatin ta sanya.

A irin jawaban da jama'a kan yi idan suka haɗu a wajen taruruka. Su na cewa babu wanda ke inkarin jam'iyar EPRDF ba za ta kasance babbar jam'iyar da za ta yi nasara a wannan zaɓe ba. Amma mun ɗauki matakan taka tsantsan domin kariya ga abinda ya wakana a shekarar 2005. A game da yaƙin neman zaɓe kuwa, ba ƙaramin kuɗi jam'iyar take kashewa ba. Alal misali gudunmawar da ta samu daga hukumomi da ƙungiyoyi masu zaman kansu sun haura euro miliyan ɗaya da dubu ɗari biyu.

Wani ma'aikacin zaɓen na cewa "mu kan baiwa matasa ƙananan rigunan T-Shirt da bajen jam'iya domin tallatawa".

Dr. Negasso Gidada
Dr. Negasso Gidada shugaban tawagar sa ido na ƙungiyar tarayyar TuraiHoto: DW

Dr Negaso Gidadi wanda shine muƙaddashin shugaban Jam'iyar Medrek haɗaɗɗiyar Jam'iyun adawa masu rajin cigaban demokraɗiya ya yi bayani da cewa "A shekaru biyar da suka wuce an kama shugabanin adawa an tsare su a gidajen yari, ana yiwa yan adawa barazana iri iri, a taƙaice ma dai yan adawa basu da damar buɗe ofisoshi a wurare da dama, saboda haka a garemu yanayin da za mu shiga zaɓe ba abu ne da za'a ce akwai adalci a cikinsa ba.

Jam'ian ƙasa da ƙasa su kimanin 190 ne waɗanda suka haɗa da jami'an ƙungiyar tarayyar turai za su sa ido domin ganin yadda zaɓen zai gudana.Thijs Berman shine shugaban tawagar sa ido ta ƙungiyar tarayyar Turai.

"Yace a baiyane yake cewa abin da zai faru a wannan zaɓe da kuma tarzomar ta auku a shekarar 2005 na nuni da irin ƙalubalen dake gaba. A wannan karon jama'a na buƙatar zaɓe mai tsabta da kwanciyar hankali. A matsayina na babban Jami'in sa ido na ƙungiyar tarayyar turai, za mu yi aiki ne da gwamnati wadda ke da irin na ta shakku musamman game da manufar da suke ganin mun zo da ita".

Mawallafa : Ludger Schadomsky / Abdullahi Tanko Bala

Edita : Umaru Aliyu