1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓen majalisar dokoki a Sri Lanka.

April 8, 2010

An kawo ƙarshen zaɓen majalisar dokoki a Sri Lanka.

https://p.dw.com/p/MrCg
Shugaba Mahinda Rajapaksa, a lokacin da yake kaɗa ƙuri'arsa.Hoto: AP

Jami'an da suka sa ido akan zaɓen majalsar dokoki da ya gudana a Sri Lanka sun ce zaɓen ya samu halarcin masu ƙuri'u da yawansu yayi kashi 55 daga cikin ɗari inda hakan ke zaman adadi mafi ƙaranci a jerin zaɓuɓɓukan da suka gudana a wannan ƙasa tun shekara ta 1947. Hukumar zaɓen ƙasar ta ce za ta ba da sakamakon ƙuri'un da aka kaɗa akan kujeru 225 a gobe Juma'a. Wannan zaɓe ya biyo bayan sake zaɓar Shugaba Mahinda Rajapaksa ne da aka yi a farkon wannan shekara, bayan da sojojin ƙasar suka murƙushe 'yan awaren Tamil Tigers. Wasu rukunoni guda biyu na 'yan sa idon sun ce duk da kuwa tabbacin da gwamnati ta bayar masu ƙuri'u daga 'yan ƙabilar Tamil marasa rinjaye ba su samu motocin da suka yi jigilarsu zuwa runfunan zaɓe ba. 'Yan sanda da sojoji kimanin dubu 80 suka ɗauki matakan tsaron a runfunan zaɓe.

Mwallafiya: Halima Balaraba Abbas

Edita: Muhammad Nasiru Awal