1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓen majalisar dokoki a Mauritius

May 5, 2010

An gudanar da zaɓen majalisar dokoki a Mauritius.

https://p.dw.com/p/NFGM
Navinchandra Ramgoolam, framinisan Mauritius.Hoto: picture-alliance / dpa

A ƙasar Mauritius mutane kimanin dubu ɗari tara sun kaɗa ƙuri'arsa a zaɓen majalisar dokoki da ya gudana a yau Laraba. Framinista Nabichandra Ramgoolam na jam'iyyar Labour da ke mulkin ƙasar ya ƙarfafa imanin cewa shi ne zai lashe wannan zaɓe. A yakin su na neman zaɓe shi da jam'iyyar adawa ta Mauritian Militant Movement sun fi mai da hankali ne akan buƙatar samun inganci da adalcin rayuwa wa al'umar wannan ƙasa. Kasar ta Mauritius ta taka rawar gani wajen kawar da raɗaɗin matsalar tattalin arziƙi da ta addabi duniya fiye da yadda aka zata a baya ga kasancewa ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi samun ɗorewar tattalin arziƙi a Afirka . Amma kuma masharhanta sun yi imanin cewa kowanne daga cikinsu ya lashe zaɓen zai iya ci gaba da shirin yin gyare-gyaren tattalin arziƙi da zai haɗa da sassa daban-daban a maimakon ci gaba da dogaro akan sukari, masaƙu da kuma yawon buɗe ido da ke samar wa ƙasar biliyoyin kuɗaden shiga.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas

Edita: Ahmed-Tijani Lawal