Zaɓen 2011 a Najeriya
October 16, 2010Cibiyar nazarin ɗemukurɗiyya da ke Najeriya wato NDI a taƙaice ta ce ta gano an samu ci-gaba da ke ba da ƙarfin guiwa a shirye-shiryen da Najeriya ke yi na shirya babban zaɓen ƙasar a shekara ta 2011, to sai dai fa ta ce akwai sauran matsaloli masu yawa a gaba da ya kamata a shawo kansu.
Hon Joe Clark tsohon Firaministan ƙasar Canada wanda ke cikin tawagar da ta gudanar da nazari a kan shirye-shiryen da Najeriya ɗin ke yi kan zaɓen ya ce muhimmin abin sha'awa shi ne irin zummar da 'yan Najeriya suka nuna na tabbatar da samun sauyi daga yadda aka gudanar da zaɓuɓɓuka a baya, domin a samu sahihin zaɓe bisa gaskiya a 2011.
Shekaru goma sha ɗaya kenan dai cibiyar nazarin demukuraɗiyyar na gudanar da harkokin da suka shafi bunƙasawa da tallafawa mulkin demukuraɗiyya a Najeriya.
Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita: Mohammad Nasiru Awal