1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓen 2011 a Najeriya

April 12, 2010

Muƙaddashin shugaban Najeriya ya yi alƙawarin shirya zaɓe na gaskiya a shekarar 2011

https://p.dw.com/p/Mujs
Muƙaddashin shugaban Najeriya Goodluck JonathanHoto: picture-alliance/dpa

Muƙaddashin shugaban tarayyar Najeriya Goodluck Jonathan ya yi alƙawarin shirya zaɓe bisa gaskiya da adalci a shekara ta 2011 a wannan ƙasar ta Najeriya mafi yawan al'umma a nahiyar Afirka. Jonathan wanda ke ziyarar aiki a birnin Washington na Amirka, ya faɗawa majalisar hulɗa da ƙasashen waje ta Amirka cewa wannan shi ne babban burin da ya ke son cimma a cikin shekara guda. Ya ce yanzu haka yana fuskantar babban ƙalubale a rayuwarsa ta siyasa. Shi dai muƙaddashin shugaban na Najeriya Goodluck Jonathan wanda ya fara jan ragamar mulkin Najeriya bayan da shugaban ƙasa Umar Musa 'Yar Adua ya tafi neman magani a Saudiya a watan Nuwamban bara, ba ya da isasshen lokaci don tinkarar matsalolin da suka yiwa Najeriya katutu wato kamar rashin tsaro, rigingimun addini da kuma rashin shirya zaɓe na gaskiya.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Abdullahi Tanko Bala