1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓen ƙasar Brazil

October 2, 2006
https://p.dw.com/p/Buhg

Shugaban ƙasar Brazil Luiz Inacio Lula da Silva, ya gaza samun nasara a zagayen farko na ƙuriár da aka kaɗa a zaɓen shugaban ƙasa. Bisa ga sakamakon zaɓen, Lula da Silva bai sami kashi 50 cikin dari na yawan ƙuriun da ake buƙata ba. Lula ya sami kashi 49 cikin ɗari yayin abokin hamaiyar sa Alckmin yake da kashi 41 na yawan ƙuriún da aka kaɗa. A sakamakon hakan a yanzu zai sake fafatawa da babban mai kalubalantar sa Geraldo Alckmin tsohon gwamnan jihar Sao Paulo a zagaye na biyu na zaɓen a ranar 29 ga wannan watan.