1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

090410 Sudan Wahlen

April 9, 2010

Duk da janyewar da wasu 'yan adawa suka yi 'yan Sudan na fatan gudanar da zaɓukan cikin kwanciyar hankali da lumana

https://p.dw.com/p/MsDd
Shugaba al-Bashir na SudanHoto: DW/AP

Daga ranar Lahadi masu zaɓe a Sudan za su kwashe kwanaki uku suna kaɗa ƙuri´a a zaɓukan shugaban ƙasa baki ɗaya, wakilan majalisun dokokin ƙasa da na jihohi sai kuma na gwamnoni. Bugu da ƙari a kudancin Sudan za a gudanar da zaɓen majalisar dokokin yankin da na shugaba. Tun shekaru 24 da suka wuce ba a gudanar da wani zaɓen gama gari a Sudan ba saboda yaƙin basasan da aka yi fama da shi a kudancin ƙasar. Amma yarjejeniyar zaman lafiya ta shekarar 2005 ta tanadi gudanar da zaɓe kana an yi tsammanin cewa raba madafun iko zai tabbatar da zaman lafiya, to sai dai sabon zaɓen ya ta da wata sabuwar taƙaddama.

Sudan Wahlen Mann mit Flagge in Khartoum
Zaɓe a SudanHoto: AP

Chan Lol babban sakataren majalisar majami´un Sudan ya bayyanan zaɓukan da cewa abin tarihi ne wanda tun watanni da dama da suka wuce yake ɗaukar kanun labaru. Majami´un dai za su tura masu sa ido a zaɓe zuwa tashoshin zaɓe. Kuma tun ba yau ba majami´un suka yi ta gabatar da tarukan wayarwa da jama´a  kai game da muhimmanci da kuma yadda zaɓukan za su gudana, inji Chan Lol.

"Zaɓukan za su bawa mutanen da ba su taɓa kaɗa ƙuri´a a rayuwarsu ba sanin yadda hakan ke gudana. Ya na nuni da yadda zaɓe na demokuraɗiyya ke gudana ko da yake da akwai 'yan kura-kurai a ciki."

Da yawa daga cikin masu zaɓen ba su taɓa tsayawa gaban tashar zaɓe ko riƙe takardar zaɓe a hannu ba. Shekaru 24 ba a gudanar da zaɓe a kudancin Sudan ba saboda mummunan yaƙin basasa tsakanin 'yan tawayen ƙungiyar 'yantar da kudancin ƙasar da sojojin gwamnati da aka yi fama da shi a kudancin Sudan ɗin. Duk da cewa yanzu zaman lafiya ya samu a yankin amma ba kowa ne ɗan Sudan ne zai kaɗa ƙuri´a ba, musamman a yankin Darfur, inda ƙungiyoyin 'yan tawaye ke yaƙi da sojojin gwamnati da 'yan bangan Janjaweed, rikicin da ya ta da miliyoyin mutane daga yankin. Jacky Marmour na wata ƙungiyar agaji ta ƙasar Faransa ne dake aiki a Darfur cewa yayi:

Flüchtlingslager im Darfur
Sansanin 'yan gudun hijira a DarfurHoto: picture-alliance/ dpa

"Ba ma cikin halin da mazauna a Darfur za su iya shiga cikin wannan zaɓe. Ban da haka mutane da yawa a sansanonin 'yan gudun hijira sun ƙi a yi musu rajista domin hakan na nufin kenan sun amince sansanonin gudun hijirar sun zama mazauninsu."

Su ma ƙungiyoyin kare haƙin Bil Adama sun rawaito cewa ba a yiwa wasu 'yan ƙasar rajista ba. Domin gwamnati ta gano cewa bayan yaƙin basasa na tsawon shekaru, waɗannan mutane za su goyawa 'yan adawa baya.

Hatta a kudancin Sudan ɗin ma ba kowa ne zai je tashar zaɓe ba saboda rikice rikice na ƙabilanci. Alal misali a bara yawan mutanen da suka rasa rayukansu sun fi na Darfur. Masu lura da al´amuran yau da kullum na ciki da wajen Sudan na zargin gwamnati da yunƙurin yin maguɗi. A saboda haka wasu manyan jam'iyun adawa suka ƙauracewa zaɓen. Muu Thiik na gidauniyar Friedrich-Ebert ya nunar da dalilan jam´iyun da cewa.

"Akwai wasu dokoki da ba a soke su ba. Misali dokar tabbatar da doka da oda wadda za ta hana gudanar da zaɓe cikin adalci. Ga kuma dokokin tsaro da na watsa labaru da har yanzu ba a canza su ba. Saboda haka jam'iyun adawa ke fargabar cewa ba za a gudanar da zaɓen cikin gaskiya da adalci ba."

Su ma ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa na zargin gwamnatin Sudan a birnin Khartoum da hukumomin yankin cin gashin kan kudancin ƙasar da amfani da waɗannan dokokin don yin aringizon ƙuri´u.

To sai dai duk da haka ɗaukacin 'yan ƙasar na fatan cewa zaɓen zai gudana cikin kwanciyar hankali da lumana, domin zama zakaran gwajin dafi na ƙuri´ar raba gardama da za a gudanar a baɗi kan bawa kudancin ƙasar 'yancinsa.

Mawallafa: Daniel Pelz/Mohammad Nasiru Awal

Edita: Umaru Aliyu