1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓen ƙananan hukumomi a Britaniya

May 5, 2006
https://p.dw.com/p/BuzZ

Jamíyar Labour ta P/M Britaniya Tony Blair, ta sha kaye a zaɓukan kananan hukumomi da aka gudanar a faɗin ƙasar. Sakamakon farko ya nuna jamíyar adawa ta Conservative ta sami gagarumin rinjaye. Ita ma dai jamíyar BNP ta yan jari hujja ta tagaza a zaɓen wadda masu kaɗa kuriá suka yiwa jamíyar labour lugude tun daga tushe, jamíyar da ta shafe shekaru goma tana jagorancin gwamnatin Britaniya. Manazarta na baiyana cewa sakamakon zaɓen wanda bai zo wa jamíyar ta labour da dadi ba, zai tilastawa P/M Tony Blair ya yiwa gwamnatin sa garanbawul. Bugu da kari yana kuma fuskatntar matsin lamba a buƙatar da ake masa ta baiyana takamammen lokacin da zai yi murabus.