Zaɓe a Timor ta gabas
April 9, 2007Talla
Yau ne al´ummomin yankin gabacinTimor, su ka shirya zaɓen shugaban ƙasa.
Rahotani daga ƙasar sun nunar da cewa, mutane masu yawa sun kaɗa ƙuri´a, sannan an gudanar da zaɓen lami lahia duk ruɗani da fargaba da ke zukatan jama´a,kamar yadda Praministan ƙasar Jose Ramos-Horta yayi hasashe kamin fara zaɓen.
Saidai Hukumar zaɓe mai kanta ta ƙasa, ta koka da ƙaranci takardun zaɓe, to amma a cikin ɗan lokaci ƙanƙane jiragen sama masu dura angulu, na Majalisar Ɗinkin Dunia su ka magance wannan matsala.
Wannan shine zaɓen farko, da al´ummomin ƙasar su ka yi, tun bayan samun yancin kanta, a shekara ta 2002.
Shugaban mai ci y