1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓe a RDC

Yahouza S.MadobiJuly 25, 2006

Saura ƙiris a fara zaɓen shugaban ƙasa da na yan majalisun dokoki a Jamhuriya Demokradiyar Kongo

https://p.dw.com/p/Btyt
Hoto: PA/dpa

Ranar lahadi mai zuwa idan Allah ya kai mu ake, gudanar da zaben shugaban ƙasa da na yan majalisun dokoki, a Jamhuruiya Demokradiyar Kongo.

A jimilce yan takara 33 ke neman maye kujera shugabancin ƙasar, a ɓangaren Majalisa yan takara kussan dubu 10,su ka shiga gwagwarmayar zama a Majalisar Dokoki, mai kujeru 500 daidai.

Baki ɗaya mutane fiye da million 25 ya cencenta su ka kaɗa ƙuri´a a runfunan zaɓe dubu 50, dake warwatse a faɗin ƙasar, wadda mizanin girman ta, ya kai addadin yawan ƙasashen yamacin turai baki ɗaya.

A na sa ran zaɓɓuɓkan na ranar lahadi mai zuwa, za su kawo ƙarshen mulkin riƙwan ƙwarya na tsawan shekaru 3, da aka girka, bayan yaƙin bassassa na tsawan shekaru 5, da ya ɗaiɗaita wannan makekiyar ƙasa, mai maƙwabtaka da ƙasashe 9 na Afrika.

Zaɓen shine irin sa na farko, tun bayan da tsofuwar Zaire, ta samu yancin kanta, daga turawan mulkin mallaka na ƙasar Belgium.

A tsawan shekaru 32, Mareshal Mubutut Sese Seko, ya ja ragamar Zaire, cikin mulkin danniya da kama karya.

Saidai duk da haka masharahanta, sun ruwaito cewar ya cimma babbar nasara, ta fannin samar da dunƙullaliyar ƙasa, saɓanin magabatan da su ka biwo bayan sa.

Masu kulla da harakokin siyasa, a Jamahuriya Demokraɗiyar Kongo na hasashen cewa, daga jerin yan takara 33, shugaban riƙwan ƙawyra Joseph Kabila, wanda ya gaji uban sa, Laurent Desire Kabila, da akayi wa kissan gilla a shekara ta 2001 ya fi nuna alamun lashe zaben, ko da ya ke dai, ba an san maci tuwo ba, sai miya ta ƙare.

Joseph Kabila mai shekaru 35 a dunia, na kurin cewar, ya taka rawar gani ta fannin maido da zaman lahia a Jamhuriya Demokradiyar Kongo, sannan ya cika alkawarin da ya ɗauka na shirya zaɓe bisa tafarkin Demokraɗiya.

A watan juni da ya gabata, Joseph Kabila ya girka hadin gwiwar jam´iyu 31, wanda za su goya masa baya, a zabbuka, da burin cimma nasara tun zagaye na farko.

Shugaban riƙwan ƙwaryar, zai fafata da sauran yan takara da su ka haɗa da 2, daga mataikan sa, wato Jean Pierre Bemba, da kuma Azarias Ruberwa, dukan su tsafin shugabanin ƙungiyoyin tawaye.

A watan yuni ne, shima Jean Pierre Bemba ya samu goyan baya daga gungun jam´iyun siyasa 23.

Ya na tinkafo, da kyaukyawan aikin da ya gudanar, a lokacin da ya jagoranci hukumar tattalin arziki ta kasa, ta la´kari da ƙwaƙwara shaidar da ya samu daga al´umma.

Saidai babbar jam´iyar adawa ta UDPS, ta bayana ƙauracewa zaɓen domin a cewar ta, ya na cike da magudi.

Daga cikin yan takara shugaban ƙasa akwai Nzanga Mobutu ɗaya daga cikin yayan Guy Patrice Lumumba.

A yayin da ya rage kwanaki 15 aka shirya wannan zaɓe 15 daga cikin yantakara sun bayyana ƙaurace masa, to saida masu sa ido daga ƙasashen turai sun nunar da cewa, kassasun yan takara sun ɗauki wannan mataki, dalili da rashin issasun magoya baya.

Wakilin mussamman na kungiyar gamayya turai a yankin Grands Lacs, Aldo Ajello, ya bayyana mahimancin shirya zaɓe cikin nasara a Jamhuriya Demokradiyar Kongo.

Ajello ya ce Kongo ƙasa ce, ɗaya tamakar da 10, ta fannin girma, barkewar tashin hankali a cikinta ko shaka babu, kamar yada a ka gani zai ɓulla a sauran ƙasashe 9 da ta ke iyaka da su, a game da haka ya zama wajibi a kimsta wannan ƙasa don cimma kwanciyar hankali mai ɗorewa a yankin baki ɗaya.