1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

150910 Wahl Elfenbeinküste

Halimatu AbbasSeptember 15, 2010

A ranar 31 ga wannan wata na Oktoba ne za a gudanar da zaɓe a Abirkos.

https://p.dw.com/p/PCzK
Shugaba Laurent Gbagbo.Hoto: Public Domain

Tun bayan mutuwar Shugaba Houphouet Boigney  a tsakiyar shekarun 1990 ne,  ƙasar Abirkos ta tsunduma a cikin  rikici . To sai dai a yanzu duniya baki ɗaya ta zura mata ido, domin ganin ko shin zaɓen da zai gudana a ƙasar a ranar 31 ga wannan wata na oktoba zai samar da mafita daga rikicin ƙasar da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa.

Elfenbeinküste Militär Oberst Bamba
Sinima Bamba, na ƙungiyar 'yan tawayen New Forces tare da Ute Schaeffer, ta Deutsche Welle.Hoto: DW

Sakataren  ƙungiyar 'yan tawayen New Forces ta Abisrkos; Sinima Bamba  ya bayyana fatansa na gudanar da zaɓe kafin ƙarshen watan nan na Oktoba inda yake cewa: "Fatan ɗokacin al'umar ƙasar nan ta Abirkos shi ne samun zaman lafiya . Mun gaji da yaƙi da bai kamata ce an shafe sama da shekara guda ana gwabzawa  ba. Amma sai gashi  an shafe  har shekaru takwas.  Kowa ya samu rabonsa daga wannan yaƙi, wanda a dalilinsa aka ta jinkirta fid da jadawalin  gudanar da zaɓe."

Tun bayan zaɓen shekarar 2000 ne dai 'yan tawayen new Forces suka ƙaddamar da yaƙi akan shugabannin ƙasar ta Abirkos a shekarar 2002, da ya haifar da raba ƙasar gida biyu, ɓangaren arewa a hannun 'yan tawaye da ɓangaren kudu a hannun dakarun gwamnati.

Jean Louis Billon Industrie-und Handelskammer Elfenbeinküste
Jean Louis Billon.Hoto: Ute Schäffer

ƙasar ta Abirkos dai ta fuskanci koma bayan tattalin arziƙi a shekarun da suka gabata. Jean Louis Billon, shugaban ƙungiyar masana'antu da kasuwanci a ƙasar ya nuna irin illar da hakan ya yi ga tattalin arziƙin kasar. Ya ce: "Fatan baki ɗayanmu al'umar Abirkos; shi ne samun mafita daga wannan rikici,  saboda cewa 'yan kasuwa da al'uma musamman matasa ne wannan rikici ya fi shafa. Akwai matasa miliyan huɗu da ke rashin aikin yi, sakamakon ragargajewar ƙananan sana'o'i da suke yi a da. Akwai kuma wasu su miliyan huɗu da ba su taba samun aikin yi ba. Kenan muna da matasa da yawansu ya yi miliyan takwas da ke rashin aikin yi. Wannan dai abu ne mai ban tsoro."

Tun a shekarar 1990 ne dai 'yan takara a zaben ƙasar ta Abirkos ke yaƙin neman zabe. Waɗannan sun haɗa ne da Shugaba Laurent Gbagbo, mai ci yanzu da  tsohon Shugaba Konan Bedie da kuma Alessane Dramane Ouatarra, wadanda aka dade ana damawa da su a siyasar ƙasar- da aka ganin cewa babu wani canji da za su samar a ƙasar. Akan haka ne Jean Louis Billon ya bayyana shakkunsa game da samun mafita daga rikicin ƙasar bayan wannan zaɓe inda yake cewa:"Idan muka yi la'akari da yadda baki ɗayan al'amura ke gudana, za mu gano cewa mun yi amfani da dukkan damammakin da ke akwai na samar da zaman lafiya fiye da ma lokacin yaƙin duniya na farko da na biyu. Amma har yanzu an kasa warware wannan rikici.  A don haka ina bayyana shaku game da warware wannan rikici a siyasance.  In da a ce a gaskiya mun so gudanar da zaɓe da tuni mun yi haka."

A ra'ayin Billon dai babu wani canji da za a samu daga wannan rikici bayan gudanar da zaɓen. Za a ci gaba da ne da samun rarrabuwa kawuna tsakanin kudanci da arewacin asar, sakamakon rashin samun nasarar shirin sasantawa tsakanin 'yan tawaye da dakarun gwamnati-abin da ka iya janyo karaƙ  taɓaɓarewar tattalin arziƙin ƙasar ga baki ɗaya. Masu sa ido akan yadda al'amura ke gudana a ƙasar ta Abirkos sun ce ɓangarorin ba su da gurin kawo ƙarshen wannan yaƙi saboda ribar da kowannensu ke samu daga rikicin.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas

Edita: Ahmad Tijani Lawal