1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaá dagewa hukumar falasdinawa takunkumi idan.........

September 13, 2006
https://p.dw.com/p/Bujf

P/M Britaniya Tony Blair ya buƙaci dagewa hukumar gudanarwar falasdinawa takunkumin tattalin arziki idan sabuwar majalisar gudanarwa ta haɗin kan ƙasa da zaá kafa ta cika kaídojin ƙasa da ƙasa. Jamián Falasɗinawan na fatan sabuwar gwamnatin da zaá kafa zata share fagen ɗage takunkumin tsukewa hukumar gudanarwar falasɗinawan bakin aljihu, wanda aka ƙaƙaba mata tun bayan da Hamas ta kafa gwamnati a watan Maris na wannan shekarar.