1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yusuf Islam na ba da gudunmawa wajen kyautata zamantakewa

Mohammad Nasiru AwalJanuary 24, 2007

Yana taka muhimmiyar rawa a kokarin samar da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai dabam dabam.

https://p.dw.com/p/BvT2
A da Cat Stevens, yanzu Yusuf Islam
A da Cat Stevens, yanzu Yusuf IslamHoto: AP

Jama´a masu sauraro barkanku da warhaka, barkanmu kuma da saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na Taba Ka Lashe, shirin da ke tabo batutuwan da suka shafi al´adu, addinai da zamantakewa a sassa daban daban na duniya. An dade ba´a ji duriyar Yusuf Islam ba wanda a fagen wakoki da kade-kaden zamani cikin shekarun 1960 da 1970 aka fi saninsa da sunan Cat Stevens. To amma yanzu bayan shekaru 28, shahararren mawakin kuma mawallafi ya sake fito da sabon faifayen CD a fagen wakoki. A cikin shekara 1977 dan Birtaniya kuma mazaunin birnin London mai shekaru 58, ya musulunta, kuma tun sannan ya dukufa wajen fahimtar da jama´a game da addinin Islama. Ya gina makarantar Islamiya kuma ana girmama sa a matsayin sa na musulmi dan Birtaniya, duk da cewa shi ba limami ba ne. To shirin na yau zai duba rayuwar Yusuf Islam ne da kuma gudunmmawar da yake bayarwa a kokarin fahimtar da jama´a game da addinin Islama. Masu sauraro MNA ke lale marhabin da saduwa da a cikin shirin.

Musik.......Musik

Madalla. A cikin shekara ta 2004, lokacin da ya so shiga Amirka, jami´an shige da fice sun tsare Yusuf Islam har tsawon sa´o´i 24 kafin a mayar da shi Birtaniya. To amma shekaru biyu bayan haka, an yi masa kyakkyawar tarba sanda ya sake komawa Amirka. Domin Yusuf kamar yadda ya ke kiran kansa a yanzu, ya je Amirka ne domin, ya tallata sabon faifayen sa na CD, wato na farko a cikin shekareu 28. A wancan lokaci kuwa ya daina amsa sunan Cat Stevens, kuma ya bace daga fagen wakoki da kade kade na zamani. Ya mayar da hankalin sa ga addinin Islama, sannan a shekarar 1977 ya musulunta. Daga nan sai Yusuf Islam ya fara aikin gina makarantun Islamiya. A dangane da haka an yi ta zarginsa da marawa masu matsanancin ra´ayin kishin Islama baya.

A cikin watan desamba ma Yusuf ya bayyana a matsayin babban bako na wani shirin telebijin mai farin jini a nan Jamus. Ko da yake shirin ba na siyasa ba ne, amma Yusuf yayi amfani da wannan dama wajen yin gabatar da kansa a matsayin mai sasantawa da yin kira da zaman lafiya tsakanin al´adu da mabiya addinai dabam-dabam.

1. O-Ton Yusuf:

“Ko kadan ban koma fagen harkar wakoki ba. Ni dai ina daukar kai na a matsayin wani mai wa´azi wanda ke kokarin dinke baraka tsakanin addinai da al´adu dabam-dabam. Alal hakika abin da na ke yi kenan yanzu. Kuma bai da alaka da harkar wakoki face taimakon al´uma.”

Yusuf na matukar nuna adawa da masu kokarin haddasa gaba da rashin jituwa tsakanin al´adu da addinai. Ya ce rashin fahimta da gurguwar fassarar da dan Adam ke yi wa addini yake janyo fadawa wannan matsala. Amma addinan kan su ba su bambamta da juna ba.

2. O-Ton Yusuf:

“Idan muka bi dokokin ubangiji, zamu ga cewar dukkan Annabawa kama daga Annabi Musa, Annabi Issah har izuwa Annabi Mohammad tsira da aminci su tabbata a gare shi, sun yada kalmar Ubangiji ne. Babu daya daga cikin su da yayi magana ta radin kansa, dukkan su sun yi amfani ne da wahayin Ubangiji, shi ya sa ba´a taba samu sabani a tsakanin su ba. To mai yasa mabiyan su ke fada da juna? Suna haka ne saboda sun ki bin umarnin Annabawa, sai na wasu mutane wadanda ba su san Ubangiji ba.”

Waka tana hada kan al´uma kuma tana aikewa da wani sako mai ma´ana da ke sa mutum cikin wani hali na natsuwa, wanda watakila ba za´a iya bayaninsa a cikin rayuwa ta yau da kullum ba sai a cikin waka, inji Yusuf. Saboda haka ne ya kan yi kide kide don samar da kudin tafiyar da wasu ayyuka taimakon jama´a alal misali a Bosniya da Darfur da kuma wasu makarantun Islamiya a birnin London. A wata hira da mujallar Der Spiegel ta nan Jamus ta yi da shi, Yusuf ya ce ya kan rike wasu kudaden don amfanin kansa, domin more rayuwa akan hanyar da ta dace ba laifi ba ne.

A da an taba zargin sa da nuna goyan baya ga fatawar Ayatollah Khomeini, inda yayi kira da a kashe marubucin nan wato Salman Rushdie a game da littafin sa mai taken ayoyin shaidan. Yusuf Islam ya yi watsi da wannan zargi, inda ya ce kafofin yada labaru ne suka yi kokarin shafa masa kanshin kaji.

3. O-Ton Yusuf:

“Irin wannan salo na yiwa addinin Islama gurguwar fahimta, tamkar batanci ne ga mafi rinjayen al´uma. Idan ka tambayi ko wane musulmi ra´ayinsa zai baka irin wannan amsa. Matsalar dai ita ce wasu masu matsanancin ra´ayi sun kirkiro da nasu ra´ayin, ta yadda a na su ganin za´a daidaita duniya baki daya. Amma wane sakamako muka samu? Komai ya kara tabarbarewa. An haramta kisan kai a cikin musulunci. Saboda haka mai yasa wasu ke cewa halan ne. Ka ga an canza abin da addinin ke koyarwa. Idan ana maganar zaman lafiya wasu musulmi kan manta cewa kalmar Islam ta samo asali ne daga Salam wato zaman lafiya. To amma sun saka batutuwa na siyasa da yawa a ciki.”

Yusuf ya kara da cewa ko shakka babu musulunci kamar sauran addinai, addini ne na zaman lafiya. Saboda haka ya dukufa yanzu ba ma kawai a cikin makarantunsa na birnin London ba, a´a har ma a fagen wasanni na duniya ba ki daya wajen yada wannan manufa ta zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin al´adu da mabiya addinai dabam-dabam. Ya ce ba yana haka ba ne don neman suna ko shahara a duniya ba.

4. O-Ton Yusuf:

“Manufar addini ita ce hana mutum yiwa dan´uwansa laifi ko cin zarafinsa. Hakan kuwa ita ce manufar rayuwa, yadda mutum zai kyautatawa makwabcinsa da na kusa da shi. Bai kamata ka ci mutunci ko zarafin wani ba. Manufar rayuwa kenan, kuma hakan ta zama mini wata hanyar taimakawa mutane domin hana tashe tashen hankula. Manufar mu dai ita ce samar da zaman lafiya amma ba ta da fitina ba.”

To Allah Ya ba mu zaman lafiya a duniyar baki daya. To masu sauraro yau kuma a nan zamu yi sallama da ku a cikin shirin. A madadin YSM wanda ya taya ni gabatar da shirin, MNA ke cwea a kasance lafiya daga nan Bonn.