′Yunwa ta ɓulla a ƙasar Chadi | Labarai | DW | 05.05.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yunwa ta ɓulla a ƙasar Chadi

ƙarancin abinci ya fara addabar mazauna yammaci da kuma gabashin Chadi

default

Alamar 'yunwa a ƙasar Chadi

Wasu 'yan ƙasar Chadi sun fara ƙaurace wa muhallinsu sakamakon yunwa da ta fara addabar wasu yankunan ƙasar. Hukumar da ke kula da jin kai ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta baiyana cewa aƙalla mutane miliyon biyu sun fara fiskantar ja'ibar 'yunwa biyoywan bayan fari da Chadin ta saba fiskanta.

Majalisar ta Ɗinkin Duniya ta nunar da cewa mazauna yammaci da kuma gabashin na Chadi sun fara tsallakawa ƙasashen Sudan da kuma Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya domin samun na sa wa a a bakin salati. Sanarwar ta MDD ta nunar da cewa farashin hatsi da al´umar ƙasar ke dogaro shi yayi haihaiwar goron zabo sakamakon rashin damina mai albarka.

Gwamnatin ƙasar ta Chadi ta ƙaddamar da shirin sayar da kayayyakin matsarufi a farashi mai rahusa a yankunan da ke fama da ƙarancin abinci.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Umaru Aliyu