Yunwa na barazanar halaka dubban yara a Kongo
December 12, 2017Talla
Yaran da ke a yankin Kasai da rikici na fiye da shekara guda ya daidaita ne ke bukatar taimako wanda idan ba a dauki mataki na magance matsalar cikin gaggawa ba, za iya kai wa ga mutuwar yara akalla dubu dari hudu acewar asusun da ke kula da yara, karancin anfani gona da daruruwan jama'a da suka rasa matsuguni a sanadiyar rikicin shi ya jefa yaran cikin wannan hali. Alkaluma na nuni da cewa, asibitoci da dakunan shan maguguna akalla dari biyu da ashirin aka lalata a yayin rikicin yankin na Kasai, mutane fiye da dubu uku aka tabbatar da cewa sun mutu a tashin hankalin.