1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunwa da gudun hijira a Afirka

Lawal, TijaniOctober 20, 2008

Matsaloli na yunwa da guje-gujen hijira a nahiyar Afirka.

https://p.dw.com/p/FdgC
Wani yaro ɗan Afirka da ke fama da yunwaHoto: dpa

To madalla. Matsaloli na yunwa da guje-gujen hijira a nahiyar Afurka, shi ne ya fi ɗaukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus a wannan makon mai ƙarewa, inda zamu fara da rahoton jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung dangane da sabon halin da aka shiga, wanda ya haddasa guje-gujen hijira na dubban mutane a gabacin ƙasar Kongo. Jaridar dai cewa tayi:

"A sakamakon wata sabuwar arangama da ta ɓarke tsakanin sojojin gwamnati da dakarun wasu ƙungiyoyin 'yan tawaye guda biyu a yankin arewa maso gabacin Kongo, an ƙiyasce cewar mutane sama da dubu 15 suka kama hanyarsu da gudun hijira tun abin da ya kama daga tsakiyar watan agustan da ya wuce. Ganin yadda wannan arangama ta ƙi ci ta ƙi cinyewa ana fargabar fuskantar wata ta'asa ta kisan kiyashi a lardunan Kivu guda biyu. Daɗin daɗawa ma dai rahotanni masu nasaba da hukumar 'yan gudun hijira ta MDD kimanin mutane dubu 100 ne suka tsere daga arewacin Kivu tun daga ƙarshen watan agustan da ya wuce."

Ita kuwa jaridar Die Tageszeitung ta sake mayar da hankalinta ne akan 'yan gudun hijirar Afurka dake ci gaba da tuttuɗowa zuwa Turai, inda ta ce har yau ƙungiyar Tarayyar Turai sai lalube take yi a cikin dufu a ƙoƙarin neman bakin zaren warware wannan matsala. Jaridar ta ci gaba da bayani tana mai cewar:

"Ga alamu matsalar 'yan gudun hijirar Afurka dake tuttuɗowa zuwa nahiyar Turai tana neman zama gagara-badau ga Ƙungiyar Tarayyar Turai. Kuma ko da yake an samu raguwar adadin 'yan gudun hijirar yammacin Afurka dake bi ta tekun atlantika domin kutsawa tsuburan kanariya na ƙasar Spain daga dubu 30 a shekara ta 2006 zuwa dubu shida a halin da ake ciki yanzun, amma fa a daura da hakan an samu ƙaruwar yawan 'yan gudun hijirar dake bi ta tekun bahar-rum daga arewacin Afurka, inda bana aka samu 'yan gudun hijira dubu 23 da suka yi amfani da wannan hanya a daura da baƙin haure dubu 14 a tsawon shekarar da ta wuce."

A cikin wani nazarin da tayi jaridar Süddeutsche Zeitung ta gano cewar kimanin kashi ɗaya daga cikin bakwai na al'umar duniya ke fama da matsalar yunwa, kuma lamarin ya fi tsamari a ƙasashen Kongo da Eritrea. Jaridar ta ci gaba da cewar:

"Duniya ta sake shiga wani mawuyacin hali na matsalar yunwa, bayan 'yar sararawar da aka samu zamanin baya. Ƙasashen da matsalar ta fi tsamari a cikinsu su ne na Kongo da Eritrea da Nijer da kuma Saliyo dake kudu da hamadar Sahara. Amma fa babban ummal'aba'isin wannan ci gaba shi ne hauhawar farashin kayan masarufin da aka fuskanta, lamarin da ya sanya murna ta kusa komawa ciki dangane da fafutukar da ake yi ta yaƙar talauci a duniya. Kuma ta la'akari da rikicin ƙuɗin da ake fama da shi a yanzun ba wanda zai iya yin hasashe game da yadda lamarin zai kasance nan gaba ba."