Yunwa da cututtuka na yiwa miliyoyi a Africa barazana | Labarai | DW | 10.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yunwa da cututtuka na yiwa miliyoyi a Africa barazana

Mr Jeffrey Sachs, mai bawa Mdd shawara ta musanman yace matukar kasashen yamma basu cika alkawarurrukan da suka daukarwa kasashen Africa ba a shekara ta 2006, to babu shakka da yawa daga cikin mutanen nahiyar zasu rasa rayukan su.

A cewar Mr Jeffery, akwai miliyoyin mutane a nahiyar ta Africa dake bukatar taimakon gaggawa na abinci da kuma magunguna, a sabili da matsaloli na yunwa da cututtuka dake addabar su.

Bisa hakan, babban jami´in ya bukaci kasashen da suka yiwa Africa alkawarin basu tallafin raya kasa dasu daure wajen cika wadannan alkawarurruka, don kasashen su samu sukunin shawo kann wadannan matsaloli.

Matukar ire iren wadannan kasashen basu kawo tallafin ba a cikin gaggawa, to babu makawa a cewar Mr Jeffery da yawa daga cikin mutanen African zasu rasa rayukan su a sakamakon yunwa da kuma cututtuka.