Yunkurin ′yan fafutika ya ci tura | Labarai | DW | 05.06.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yunkurin 'yan fafutika ya ci tura

Israel ta dakatar da jirgin masu fafutika ba tare da amfani da tsinin bindiga ba ko ƙarfin tuwa ba.

default

Sojojin Isra'ila sun yi nasarar dakatar da jirgin ruwan da ke ɗauke da masu goyon bayan Palesɗinawa ba tare da amfani da ƙarfi ba. Kakakin rundunar sojojin na Isra'ila ya ce masu fafutikar ba su nuna turjewa ba, bayan da sojojin ƙundunbayar bani yahudun suka yi ma jirgin nasu ƙawanya.

Wannan jirgin da ya taso daga kasar Ireland- da kuma ke maƙare da kayan agaji ya nufi Gaza ne, a wani mataki na keta takukumin hana shiga da fita da hukumomin Tel-Aviv suka sanya ma zirin. zanga-zanga na ci gaba da gudana a sassa daban daban na duniya domin Isra'ila ta ɗage killace zirin Gaza da ta ke yi shekaru uku ke nan da suka gabata.

Shugabar hukumar kare hakkin bil adama ta MDD wato Navyi Pillay ta bayyana killace zirin na gaza da matakin da ya saɓe ma dokokon ƙasa da ƙasa. ta kuma jadadda kiranta na gudanar da bincike game da dirar miƙewa da dakarun Isra'ila suka yi ma jiragen agaji.

Mawallafi: Mouhamadou awal

Edita: Abdullahi Tanko Bala