Yunkurin warware rikicin Nuclearn Iran | Siyasa | DW | 27.02.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Yunkurin warware rikicin Nuclearn Iran

Atom

Atom

Rasha ta gabatarwa Iran wani shiri na tace mata Uranium ba tare da an tilasta mata ba,wanda yin hakan ne zai kasance mataki na farko na amince wa Tehran sarrafa sinadran Uranium dinta a Rasha.

Rashan tace yin hakan ya zamanto wajibi,domin hakan ne zai rage barazanar da harkokin Nuclearn Iran din kewa duniya,.

Akan haka ne ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya fadawa manema labaru cewa,yin haka ne kasdai zai iya kawar da barazanar da Iran din kewa sauran kasashen duniya.

Ya kara dacewa hakan na daya daga cikin wasu kaidojin da ake bukatar Iran ta cika,daga cikin wadanda aka gindaya mata har zuwa lokacinda kwararru na hukumar kula da yaduwar Nuclear ta IAEA zasu tantance ta daga zargi.

Wadannan kalamai nasa sunzo ne bayan da jamian Rashan sunyi watsi da shirin cewa Rashan na shirin taimakawa ganin cewa ,Uran ta daina fuskantar matsin lamba,inda yace har yanzu da sauran rina a kaba ,na cimma yarjejeniya tsakanin bangarorin biyu ,inda yayi gargadin cewa lokaci na neman kurewa waadin 6 ga watan Maris da aka gindaya mata.

Babban jamiin shiga tsakani na Rashan Sergei Kiriyenko ya fadawa manemas labaru cewa wannan babbar matsala ce wadda har yanzu babu abun da zaa iya fadi dangane da warware ta.

Yace yanzu lokaci na neman kurewa dukkan wata yarjejeniya da zaa cimmawea akan wannan batu,koda yake yayi fatan cewa yan kwanakida suka rage gabannin taron hukumar kula da Nulear,ana iya cimma wata yarjejeniya.

Sai dai Mr Kiriyenko yace har yanzu akwai wasu batutuwa muhimma da ya kamata acimma yarjejeniya kansu.

A hira da manema labaru da sukayi jiya lahadi a birnin Bushehr dake Iran,wadda ke zama cibiyar Nuclearn Iran ,wadda Rasha ke ginawa ,Babban jamii mai shiga tsakanina Iran ,yace bangaroprin biyu sun cimma yarjejeniyar tafiyar ta aikin.

Akarkashin wannan yarjejeniya Rasha da Iran zasu samar da tsarin hadin gwiwa na sarrafa sinadran Uranium a kasar Rasha,wanda Iran zatayi Amfani dashi wajen samarda harkokin wutan lantarki wa alummanta.

Iran dai tace tana muradin tafiyar da ayyukan sarrafa sinadran Uranium da kanta acikin kasar,batu daya razana Rasha da sauran kasashen Yammaci ,wadanda suke gabnin cewa zata iya amfani da wannan dama wajen sarrafa makamai da makamashi.Tuni dai Iran din ta hakikance cewa,tana sarrafa Ura nium din ne domin samarda wutan lantarki amma ba akasin haka ba.

A hannu guda kuma Japan zata bukaci Iran data kwantarwa da kasashen duniya ,hanlakali akan harkokin Nuclearnta,domin dakatar da takunkumin da MDd ke shirin kakaba mata.Japan zata gabatar da wannan kira nata ne a yayin wata ziyarar aiki na kwanaki 3 da ministan harkokin waje Manouchehr Mottaki,ke fara gudanarwa ayau a wannan kasa.

Wannan rangadin aiki dai yazo ne yini guda ,bayan rahotanni dake nuni dacewa an cimma yarjejeniyar hadin gwiwa na sarrafa sinadaran uranium tsakanin Rasha da Iran.

 • Kwanan wata 27.02.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu1Q
 • Kwanan wata 27.02.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu1Q