1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunkurin tsige shugaban kasar Malawi

Yahouza SadissouOctober 19, 2005

Yan majalisar dokokin kasar Malawi sun shiga yunkurin tsige shugaban kasa Bingu wa Mutharika

https://p.dw.com/p/Bu4o

Majalisar dokokin kasar Malawi, ta shiga wani yunkuri na tsige shugaban kasa Bingu wa Mutharika, da ta ke tuhuma da karbar rashawa.

A wani gamen katari wannan yunkuri ya wakana a ranar da kungiyar Transpary International, ta gabatar da rahoton ta na shekara shekara, a game da cin hanci da rashawa, inda a bana ma, kasashen Afrika su ka rike matsayin su ,na sahun gaba, ta wannan mumunar dabi´a, da ke daya daga tubalin farko, na dawwamar da talauci a wannan nahiya.

Yan adawa ne, da farko su ka gabatar wa majalisa bukatar gudanar da kwaskwarima ga kundin tsarin mulkin kasa, ta hanyar kutsa ayar doka, mai bada damar, tsige shugaban kasa idan a ka same shi da lefin cin amanar kasa.

Bayan kada kuri´a a kan wannan doka, ta samu shiga a majalisa, abinda masharahanta ke dauka, tamkar matakin farko na tsige shugaban kasar Malawi.

Yan adawa da ma wasu, daga yan majalisa na jam´iyu masu rike da mulki, na zargin shugaban kasar, da rabda ciki da dukiyar jama´a.

Sannan su na tuhumar sa, da take dokokin kasa, a sakamakon murabus da ya yi daga jamiyar sa ta UDF, ya kuma kirkiro wata sabuwar jam´iya.

Ta hanyar wannan sabuwar doka, da majalisar ta rattaba hanu a kai , kakakin majalisa ya samu cikkaken yancin gurfanar da shugaban kasa,a gaban majalisa, ta kuma yanke shawara hukunci tsige shi, ko kuma barin sa, a karagar mulki.

A na sa ran, nan da dan lokaci mai zuwa, hakan zata abkuwa, kuma idan a kayi la´kari da yadda yan majalisar na adawa da masu mulki ,su ka yi tsintsiya madaurin ki daya, babau mamaki su samu nasara tube shugaban.

Saidai kungiyoyin bada agaji na kasa da kasa, da Britania da ke sahun gaba, ga kasashen da ke bada tallafi, ga Malawi sun yi kira ga yan siyasar, da su dakatar da wannan cacar baka, marassa fa´ida, su dukufa wajen samun mattakan magance matsalar balla´in yinwa da ke addabar al´umma kasa.

A karshen makon da ya gabata ne, shugaban kasar Malawi, ya bayana wa dunia cewa, kasar sa na cikin mummunan billa´in yinwa, ya kuma tara kokwan bara, ga dukan kasashe masu hannu da shuni, da kungiyn bada agaji, domin su kawo taimako cikin gaggawa.

Kiddidighar da a ka gudanar bayan bayan nan ,a kasar ta bayana cewa, a sakamakon karacin ruwan sama a tsawon shekaru da dama, da yaduwar cutar kanjamaw a kasar,a kalla mutane million 5 ke fama da matsanaciyar yinwa a Malawi daga jimmillar mutane million 12.