1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yunkurin ta'addanci ya ci tira a Beljiyam

A cewar shugaban 'yan sanda a garin Antwerp mutumin da ya yi wannan yunkuri ya fito daga kasashe da ke a Arewacin Afirka.

Jami'an tsaro a kasar Beljiyam a ranar Alhamis din nan sun yi nasara ta cafke wani mutum da ya yi kokari na kutsa kai cikin jama'a da suka fita rukunin shaguna dan yin cefane a birnin Antwerp, kamar yadda shugaban 'yan sanda a wannan birni ya bayyana.

A cewar shugaban 'yan sanda a wannan gari Serge Muyters mutumin da ya yi wannan yunkuri ya fito daga kasashe da ke a Arewacin Afirka.
Wannan dai na zuwa ne kwana guda da kai hari ta hanyar amfani da mota da wuka a Birtaniya abin da ya yi sanadi na rayukan mutane uku kuma kwana guda bayan cika shekara guda  da harin birnin Brussels wanda ya yi sanadi na rayukan mutane 32.