Yunkurin shigar Turkiya Ƙungiyar tarayyar Turai | Labarai | DW | 14.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yunkurin shigar Turkiya Ƙungiyar tarayyar Turai

Shugaban hukumar tarayyar Turai Jose Manuel Barrroso ya yi kashedin cewa shawarwarin shigar Turkiya ƙungiyar tarayyar Turai ka iya ɗaukar tsawon shekaru kimanin goma sha biyar. A hirar da ya yi da wata mujalla Die Welt ta nan Jamus, Barroso ya kuma ja hankali ga dogon burin da ake dorawa ga ƙasar Jamus wadda zata ƙarbi shugabancin ƙungiyar tarayyar Turan a cikin watan Janairu na shekara ta 2007. Yace bai kamata a ɗora buri ga Jamus ta warware dukkan matsalolin ƙungiyar tarayyar turai ba.