Yunkurin sasanta rikicin Siriya | Labarai | DW | 02.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yunkurin sasanta rikicin Siriya

Sakataren harkokin kasashen ketare na Amirka John Kerry ya bude taro kan sasanta rikicin kasar Siriya a birnin Geneva.

Taron dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da ake fama da wani dauki ba dadi a birnin Aleppo na kasar ta Siriya. A yayin wata ganawa da ya yi da takwaransa na kasar Saudiya Adel al-Jubeir da kuma babban jakadan Majalisar Dinkin Duniya a Siriya Staffan de Mistura, Kerry ya ce suna ci gaba da tattaunawa kullum domin ganin an samar da mafita, kuma yana ganin akwai haske:

"Muna daf da kai wa ga fahimtar juna, sai dai muna da jan aiki a gabanmu, shi ne dalilin da ya sa muka sake hallara a nan."


Kerry ya kara da cewa a yanzu haka suna yin iya kokarinsu domin ganin an rage tashin hankalin da ake tsaka da fuskanta a birnin na Aleppo.