Yunkurin karshe na shawo kan Iran kafin taron hukumar kare yaduwar nukiliya | Labarai | DW | 24.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yunkurin karshe na shawo kan Iran kafin taron hukumar kare yaduwar nukiliya

Tawagar masu binciken nukiliya na Majalisar Dinkin Duniya ta kama hanyatsa yau zuwa kasar Iran domin baiwa kasar damar karshe ta bada hadin kanta ga masu bincike kafin taro majalisar game da shirinta na nukiliya da zaa yi ranar 2 ga watan fabrairu.

Jamian diplomasiya sunce yanzu ya ragewa Iran ta bada bayanan da suka dace game da bincikenta na nukiliya.

Tawagar mai mutum 6 karkashin jagorancin mataimakin darekta na hukumar kare yaduwar nukiliya ta kasa da kasa Ollie Heinonen,zata bukaci kasar Iran data amsa wasu muhimman tambayoyi 5,da suka hada da bukatar duba wani yanki na sojin Iran,da batun hulda ta kasuwar nukiliya ta bayan fage da kuma tambayoyi game da shirin kera makaman nukiliya.

Ana sa ran tawagar zata mika rahotanta kafin taron na watan fabrairu.