Yunkurin dakile kwararar bakin haure | Labarai | DW | 11.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yunkurin dakile kwararar bakin haure

Shugabannin kasashen Turai na ganawa da takwarorinsu na Afirka domin hada karfi waje guda tare da shawo kan matsalar kwararar bakin haure zuwa nahiyar ta Turai.

Taron shugabannin EU da na Afirka

Taron shugabannin EU da na Afirka

Da ta ke jawabi a yayin taron shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel cewa ta yi makasudin taron shi ne hada kai da Afirka domin kawo karshen ayyukan safarar mutane da shigowa Turai ta haramtacciyar hanya. Merkel ta kara da cewa:

"Ina ganin wannan tattaunawa da musayan ra'ayi na da matukar amfani, yana da amfani wajen kawo karshen masu safarar mutane. Wannan shi ne muhimmin abin da za mu mayar da hankali a kai, mu samu kyakkyawar dangantaka tsakaninmu da Afirka, dangantakar da baya ga tallafi za ta hadar da bukatu da kuma fata."

Shugabannin kasahen kungiyar EU dai sun amince da ba wa kasashen Afirka agajin kudin Euro sama da biliyan uku domin shawo kan matsalar bakin hauren. Sai dai shugaban kasar Senegal Macky Sall ya ce ba ya son jin ana ambatar kalmar agaji, ya ce ya yadda Afirka za ta bukaci taimako wanda ya kamata ace EU ta bayar, sai dai suna bukatar hadin kai wajen shawo kan wannan matsalar domin ba bukatar kasashen Afirka bane turo yaransu zuwa Turai a matsayin bakin haure.