Yunkurin bunkasa harkokin kiwo a nahiyar Afirka
February 27, 2017A Jamhuriyar Nijer wasu shugabannin kungiyoyin makiyaya da na mazauna karkara ne daga wasu kasashe na yammacin Afirka ke halartar wani taro don duba batun matsalolin da makiyaya da ma mazauna karkara ke fuskanta a wannan lokacin na rani.
Batutuwan tsaro,na shige da ficen makiyaya da na mazauna karkara tsakanin kasashen yammacin Afirka uwa uba da rashin ingantaciyyar ciyawar dabbobi na daga cikin batutuwan da suka mamaye taron wanda shi ne irinsa karo na farko da ake yi a Nijar.Kimanin gibin tan miliyan 12 na ciyawar dabbobi ne dai gwamnatin ta Nijar ta ambaci ta ke bukata a wannan shekarar don tinkarar matsalolin na kiyo.A farkon watan gobe ne dai kungiyoyin suka ayyana da cewar za su gamu a birnin Abuja na tarayyar Najeriya don ci gaba da tattauna wannan batu.